28 Agusta 2021 - 11:21
Venezuela Ta Danganta Takunkuman Amurka Da Cin Zarafin Bil Adama

Kasar Venezuela, ta bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, data gudanar da shari’a game da takunkuman da Amurka ta kakaba mata tun cikin 2015, wadanda take dangantawa da cin zarafin bil adama.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : A ranar 23 ga wata nan ne gwamnatin Venezuela dake yankin latin Amurka, ta gabatar wa da kotun ta ICC, wani rahoto kan irin ta’adin da takunkuman Amurka suka haifar wa tattalin arzikin kasar.

Da take sanar da hakan mataimakiyar shugaban kasar, Delcy Rodrigez, a wani taron manema labarai, ta ce rahoton, mun nuna yadda al’ummar Venezuela suka shiga kunci rayuwa saboda takunkuman Amurka dama kawayenta.

Amurka dai ta tsananta takunkuman ta kan Venezuela ne, a shekarar 2016 da kuma 2017, bayan da ta kalubalanci zaben majalisar dokokin kasar.

Takunkuman da Amurka ta kakaba wa Venezuela, sun hada da haramta mata yin hulda da kamfanonin Amurka, sai kuma hana ta sayar da man fetur dinta a kasuwanin duniya, wanda kuma shi ne kahsin bayan tattalin arzikinta.

342/